Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: An gudanar da Muzaharar Ashurar Imam Husaini As tare da halartar miliyoyin mutane a fiye da garuruwa 100 a Najeriya. Wannan taruka sun gudana ne bisa ƙoƙarin "Harkar Musulunci ta Najeriya" a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Ya'qub Zakzaky HF, baya ga garuruwa daban-daban na wannan ƙasa, a wasu ƙasashe maƙwabta ma sun gudanar da shi.
A cewar rahotanni, an gudanar da tarukan a garuruwa daban-daban da safe ko da yamma, kuma sun ƙare cikin yanayi na natsuwa, tsari da haɗin kai.
Mahalarta daga matakan shekaru daban-daban, ta hanyar rera take, waƙoƙin makokin Ashura, sun nuna ƙaunarsu ga Aba Abdillah Husain (A.S) da Ahlul-Bayt (A.S).
Masu makokin kuma, tare da riƙe tutoci masu taken "Labbayka ya Husain (A.S)" da hotunan wasu shugabannin gwagwarmayar tsayin daka da farkawa ta Musulunci, ciki har da Imam Khomeini (R.A), Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i, Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, Shahid Qasem Soleimani, Ayatullah Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i da Sheikh Ibrahim Zakzaky, sun jaddada ci gaba da tafarkin yunkurin Husaini As da kuma tabbatuwa da riko ga manufofinsa.
………………………………
Your Comment